ABNA24 : A ranar 22 ga watan Yulin nan ne kungiyar tarayyar Afrika ta sanar da dawo wa da Isra’ila matsayin bayan tsawon kusan shekaru 20 na dakatar da ita.
Saidai a halin da ake ciki lamarin bai yi wa kasashen Afrika ta Kudu da Aljeriya dadi ba.
Kasashen sun yi watsi da matakin wanda suka ce babu wata hujjar yin hakan.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu, ta fitar ranar Laraba, ta danganta matakin na kwamitin kungiyar tarayyar Afrika da ‘’matakin marar dacewa’’ wanda kuma aka dauke shi ba tare da tuntubar mambobin kungiyar ba.
Kasar Aljeriya ma ta fitar da irin wanan sanarwa inda ta ce an dauki matakin ba tare da tuntubar mambobi ba.
342/